Taron MajalisarƊinkin Duniya akan Siriya
July 19, 2012Talla
Ƙasahen guda biyu sun kawo tarnaƙi ga yunƙurin ƙasashen duniyar na ƙaƙaba wa Siriya takunkumi. Jakadin Faransa a Majalisar Ɗinki Duniya Gerar Araud, ya ce wannan al'amari, zai kawo tsaiko ga shirin zaman lafiya na Kofi Annan, sannan ya ƙara da cewar.''ya ce a yanzu ƙaraƙara ta ke, Rasha na son bai wa hukumomin ƙasar Siriya ƙarin lokaci domin murkushe yan adawa baki ɗaya.
A cikin ƙasashe 15 menbobi kwamitin, kasashe 11 ,suka kaɗa ƙuria'a amincewa da ƙudirin, yayin da Pakistan da Afirka ta kudu suka ƙauracewa ƙuria'ar.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu