1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Majalisar Ɗinkin Duniya akan Libiya

March 17, 2011

Kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinki Duniya zai tattauna batun yiwuwar ɗaukar mataki akan ƙasar Libiya

https://p.dw.com/p/10awL
Hoto: picture alliance/landov

 kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya zai kaɗa ƙuria akan daftarin dokar da zai bada damar sakawa jiragen yaƙi sama na  ƙasar Libiya takumkumi yin  shawagi a sararin samaniyar ƙasar. Jakadiyar Amerika a Majalisar Dikin Duniya Suzane Rice ta yi gargaɗin cewa kammata  ya yi kwamitin ya ɗau matakin da ya fi karfin hakan.

Sai dai kuma masu aiko da rahotannin sun ce kawo yanzu a kwai rarabuwar kawuna tsakanin menbobin kwamitin sulhu dangane da batun saka dokar ta harmcin zirga zirga.Yanzu haka dai kuma a fagen daga faɗa na ƙara rincaɓewa yayin da kanal Gaddafi ya ce a yau Alhamis dakarun sa za su ci garin Misirata da yaƙi ta kowane hali.Gaddafi dai ya ce babu maganar neman sulhu domin tattaunawa da 'yan tawaye,ya kuma shaidda cewa nan da kwanaki biyu sojojin sa za su sake kwace iko da yankunan da ke cikin hannu 'yan adawa. Babban sakataran Majalisar Dinkin duniya Ban Ki Moon ya kira da aka kawo ƙarshen zubda jini da ake yi a ƙasar.

Mawallafi:Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar