1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron MajalisarƊinkin Duniya akan Siriya

July 19, 2012

A karo na ukku ƙasashen China da Rasha sun yi amfanin da ƙarfin faɗa a ji da suke da shi wajan hawa kujerar naƙi a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya

https://p.dw.com/p/15bfx
ARCHIVBILD: The United Nations Security Council meets as current U.N. Security Council President and British Ambassador to the U.N. Lyall Grant reads a "Presidential statement" agreed to by the Security Council, including Russia and China, on Syria that backs U.N.-Arab League envoy Kofi Annan's bid to end violence that has brought the country to the brink of civil war, at U.N headquarters in New York March 21, 2012. The statement also threatens Syria with "further steps" if it fails to comply with Annan's six-point peace proposal, which calls for a cease-fire, political dialogue between the government and opposition, and full access for aid agencies. REUTERS/Mike Segar (UNITED STATES - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Ƙasahen guda biyu sun  kawo tarnaƙi  ga yunƙurin ƙasashen duniyar na ƙaƙaba wa Siriya takunkumi. Jakadin Faransa a Majalisar Ɗinki Duniya   Gerar Araud, ya ce wannan al'amari, zai kawo tsaiko ga shirin zaman lafiya na Kofi Annan, sannan ya ƙara da cewar.''ya ce a yanzu ƙaraƙara ta ke,  Rasha na son bai wa hukumomin ƙasar Siriya  ƙarin lokaci domin murkushe yan adawa baki ɗaya.

A cikin ƙasashe 15 menbobi kwamitin, kasashe 11 ,suka kaɗa ƙuria'a amincewa da ƙudirin, yayin da Pakistan da Afirka ta kudu suka ƙauracewa ƙuria'ar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita        : Umaru Aliyu