1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kawayen Ukraine

Usman Shehu Usman
October 5, 2023

Kimanin shugabannin Turai 50 na gudanar da taro a kasar Spain, inda suke kara jaddada goyon bayansu ga kasar Ukraine a yayinda yakin da Rasha ta kaddamar ke ci gaba da tsawaita.

https://p.dw.com/p/4XAmu
Granada Treffen Scholz und Selenskyj
Hoto: UKRAINIAN PRESIDENTIAL PRESS/AFP

Shugabannin da ke halartan taro karkashen wata kungiya da suka kira European Community Forum wace aka kafa watan Febrairu bayan da Rasha ta kaddamar da hari kan Ukraine, an kafa ta domin duba makomar tsaron Turai. Duk da cewa kungiyar na bada goyon bayan kudi da makamai ga Ukraine, amma kawo yanzu Ukraine ta gaza girgiza Rasha daga yankunan da Rasha ta mamaye. A cewar masharhanta, hadin kan kasashen na Yamma wajen taimakawa Ukraine yana fara samu babbar baraka, musamman daga cikin gidan kasashe irinsu Amirka da Jamus da sauransu. Ko da a safiyar wannan Alhamis, wata mijiya daga fadar gwamnnatin Jamus ta sanar da cewa shugaban gwamnati Olaf Schulz ba zai mika wa Ukraine, makamai masu linzami kirar Jamus da Ukraine ke ta neman a aika mata ba. Jami'in ya ce za a duba batun amma sai wani lokaci nan gaba.