1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kasashen Larabawa kan Siriya

July 2, 2012

Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa ya bukaci girka sabuwar gwamnati a Siriya domin samun mafita daga rikicin kasar

https://p.dw.com/p/15Q25
Syria's President Bashar al-Assad (centre R) meets U.N.-Arab League envoy Kofi Annan (centre L) in Damascus March 10, 2012, in this handout photograph released by Syria's national news agency SANA. Annan arrived in Damascus on Saturday to press President al-Assad for a political solution to Syria's year-long uprising and bloody crackdown in which thousands of people have been killed. REUTERS/SANA/Handout (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: Reuters

 Kungiyar kasashen Larabawa da 'yan adawar Siriya sun fara gudanar da taro a birnin Alkahiran kasar Masar  domin yin amshi ga kiran da aka yi na warware rikici kasar ta SIriya a cikin limana. To sai dai babban sakataren kungiyar Nabil  Al- Arabi ya yi kashedin cewa babu wani ci gaba da za a samu face an tsai da jadawalin samun sauyin gwamnati a kasar. Al -Arabi ya kuma ambaci kudurin Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci daukar matakin soji domin ba da kariya ga farar hula. 'Yan adawa sama da 200 da ke halartan taron  sun yi kira ga Al-Arabi da a daidata kan shata makomar kasar ta Siriya. 

To sai dai 'yan tawayen kungiyar Free Syria Armee da ke yaki domin 'yantar da kasar sun ki halartan taron suna masu kafa hujjar cewa mai yiwuwa ne taro ya nuna rashin amincewa da tsoma bakin sojojin ketare  da za su ba da kariya ga jama'a. Sun kuma nunar da cewa babu wani mataki da za a dauka na kebe wurin ba da kariya ko ba da gaji ko kuma ba su makamai.

 Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Saleh Umar Saleh