1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tsaro na Asiya a Singapore

Zainab Mohammed Abubakar
June 2, 2023

Taron na Singapore zai mayar da hankali kan takaddama da ke tsakanin Amurka da China da mu'amalar soji a bayan fage da diflomasiyya.

https://p.dw.com/p/4S7d4
Verteidigungsminister USA China
Hoto: Chad J. McNeeley/Department of Defense/UPI Photo via Newscom/picture alliance

Tattaunawar ta birnin Shangri-La, wacce ke samun halartar manyan hafsoshin soja da jami'an diflomasiyya da masu kera makamai da masu sharhi kan harkokin tsaro daga sassan duniya, zai gudana ne har zuwa ranar 4 ga watan Yuni a Singapore.

Firaministan Australia Anthony Albanese ne zai gabatar da jawabin bude taron a yammacin yau, gabanin jawaban da suka danganci kasuwan na sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin da sabon ministan tsaron kasar China Li Shangfu, da ake saran za su ja hankalin mahalarta.

An samu koma bayan dangantaka mafi karanci tsakanin Amurka da China a cikin shekaru da dama, yayin da manyan kasashen biyu ke ci gaba da samun rarrabuwar kawuna kan batutuwa masu yawa daga ikon mallakar Taiwan zuwa leken asiri ta yanar gizo da kuma takaddama kan yankunan tekun kudancin kasar China.