SiyasaIsra'ila
Taron G7 zai tattauna sammacin kama Benjamin Netanyahu
November 22, 2024Talla
Ministocinza su tattauna kan sammacin kama Benjamin Netanyahu da Mohammed Deif na Hamas da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar, kamar yadda firaministan Italiya Giorgia Meloni ta sanar. Wannan sanarwa na zuwa ne, bayan maganganu masu cin karo da juna daga ministoci guda biyu na firaministar. Yayin da Ministan Tsaro Guido Crosetto ya tabbatar da cewa Italiya za ta kama Netanyahu da ministansa na tsaro Gallant idan sun zo Italiyar. Mataimakin firaministan kasar Matteo Salvini, na jam'iyyar masu adawa da 'yan cirani kuma abokan kawance na gwamnatin, ya ce suna yin maraba da Netanyahu idan ya zo Italiya.