1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kare muhali a Cancun na ƙasar Mexiko

December 9, 2010

Ban Ki Moon ya yi kira da a samu haɗin kai tsakannin ƙasashen duniya a taron Cancun

https://p.dw.com/p/QUKm

Wakilai daga ƙasashe kusan 200 dake hallarta taron kare muhalli a birnin Cancun na ƙasar Mexiko, na ƙoƙarin cimma daidaito na tinkarar matsalar ɗimamar yanayi a daidai lokacin da ake shirin kammala taron a gobe Juma'a. Har ya zuwa yanzu dai akwai saɓannin da ake ci-gaba da samu tsakanin ƙasashen masu tasowa da kuma masu ƙarfin tattalin arzikin masana'antu wajen rage hayaƙin dake gurɓata sararin samaniya da manyan ƙasashen sukan fitarwa. Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi kira ga ƙasashen da su cimma matsaya ɗaya. Ƙasashe masu tasowa dai na buƙatar ganin an ƙara tsawaita yarjejeniyar Kyoto da wa'adinta ke cika a shekara ta 2012.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita: Mohammad Nasiru Awal