1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron jam'iyyar adawa ta SPD ta Jamus

December 8, 2011

Jam'iyyar SPD ta kuduri niyyar yaki da akidar kyamar baki da masu raya manufofin NAZI ke neman yada ta a Jamus

https://p.dw.com/p/13P8B
Frank-Walter Steinmeier, shugaban SPDHoto: dapd

A wani taro da suke gudanarwa a garin Wiesbaden na Jamus ministocin cikin gida na jihohi da jam'iyyar SPD ke mulki sun sake yin kira da a dauki matakin haramta jam'iyyar NPD mai manufar kyamar baki. Ministan cikin gidan jihar Rheinland Palatinate, Roger Lawentz ya ce an tsai da shawara ta bai daya a dangane da wannan bukata. Abin da ya rage yanzu shine ministocin su iya su shawo kan jam'iyyar game da hakan. A ranar 09-12-2011 ne dai ministocin cikin gidan da kuma 'yan majalisun dokoki da jihohi za su kammala wannan taro inda za su fi mai da hankali ga yaki da akidar kyamar baki. To sai dai ministan cikin gidan Jamus, Hans Peter Friedrich da sauran ministocin jam'iyyar sun yi gargadi game da daukar matakin gaggawa. A dai shekarar 2003 an shigar da bukatar kakaba haramci akan jam'iyyar ta NPD to amma sai aka kasa aiwatar da hakan kasancewar akwai shugabannin jam'iyyar da ke aiki a matsayin jami'an kare kundin tsarin mulki. Kisan ba gaira ba dalili da wasu masu raya manufofin NAZI guda uku suka aikata ne dai ya haifar da muhawara game da wannan haramci.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmadu Tijani Lawal