1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron G7 zai samar da miliyoyin yaki da gobarar Amazon

August 26, 2019

Shugabannin kasashe masu karfin arziki sun amince da samar miliyoyin euro don taimaka wa yaki da gobarar nan da ke cin kungurmin dajin nan na Amazon da ke kasar Brazil.

https://p.dw.com/p/3OVQi
G7 Gipfel in Biarritz Merkel und Trump
Hoto: REUTERS

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta ce taron kasashen nan bakwai ya dau hanyar kauce wa samun rigima dangane da shirin nan na nukiliyar Iran.

Yayin wata ganawa da 'yan jarida a taron kasashen a Faransa, Angela Merkel ta ce bakin shugabanni ya zo daya kan cewa Iran ba za mallaki makaman nukiliya ba, kuma Amirka ta yi marhabin da shirin tattaunawa tsakanin kasashen Turai da Iran.

A share guda kuwa, shugabannin kasashen sun amince da samar da euro miliyan 20, kwatankwacin dala miliyan 22, don taimaka wa yaki da gobarar nan da ke cin kungurmin dajin nan na Amazon.

Kaso mafi tsoka daga kudaden dai, za su tafi ne wajen aikawa da jiragen da za su gudanar da aikin kashe wutar, a cewar wata majiya daga fadar shugaban kasar Faransa.