1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron G20 tsakanin rikicin Siriya da kasuwar kudi

September 4, 2013

Taron a kan batun tattalin arziki, yana zuwa ne a daidai lokacin da hankalin duniya ya karkata ga rikicin Siriya da kuma rashin jituwa dake karuwa tsakanin Amirka da Rasha.

https://p.dw.com/p/19cBZ
ITAR-TASS: ST PETERSBURG, RUSSIA. AUGUST 23, 2013. Preparations ahead of G-20 Leaders’ Summit on city’s streets. St Petersburg hosts the Group of Twenty Finance Ministers and Central Bank Governors Summit on September 5-6, 2013. (Photo ITAR-TASS / Ruslan Shamukov)
G20-Gipfel in St. PetersonHoto: picture-alliance/dpa

A wannan Alhamis ake bude taron kolin yini biyu na kasashen kungiyar G20 a St. Peterburg dake kasar Rasha. Taron wanda ya kamata batutuwan tattalin arziki da na kudi su mamaye ajandarsa, yana zuwa ne a daidai lokacin da hankalin duniya ya karkata ga rikicin kasar Siriya da kuma rashin jituwa dake karuwa tsakanin Amirka da Rasha.

Shugaban Rasha Vladimir Putin bai yi shakkan kashe kudi ko nuna gajiyawa ba, don karbar bakoncin taron kolin na kasashe 20 da suka hada da masu arzikin masana'antu da masu samun bunkasar tattalin arziki da ake farawa a wannan Alhamis. Zauren taron na fadar Konstatin da ake a gabar teku na zama wani kyakkyawan kandagarki daga masu zanga-zanga. Za a yi jigilar daruruwan 'yan jarida da kananan jiragen ruwa daga St. Petersburg zuwa dandalin taron, inda daga nan za su ba da labarin taron da ke da nufin samar da karin aiki da wadata a duniya.

Tsakanin fata da zahiri

Fatan dai Putin ke nan. To amma halin da duniya ke ciki yanzu ba zai sa taron G20n karo na takwas ya tafi salin alim ba. Domin ko da yake a hukumance babu maganar rikicin Siriya a jadawalin taron, amma zai kasance wani batu da zai mamaye tattaunawar. A ranar Juma'a da ta wuce tarayyar Turai ta ce ba ta da aniyar saka batun Siriyar a kan ajandar taron, amma yanzu hatta mai masaukin bakin wato Vladimir Putin ya goyi bayan da a tattauna game da kasar ta Siriya. Sai dai ba a sani ba ko za a gana ido da ido tsakaninsa da shugaban Amirka Barack Obama. Tun bayan lamarin nan na tsohon dan leken asirin Amirka Edward Snowden dangantaka tsakanin mutanen biyu ta yi tsami.

Russia's President Vladimir Putin looks on during a meeting with journalists in the far eastern city of Vladivostok, August 31, 2013. Putin said on Saturday that it would be "utter nonsense" for the Syrian government to use chemical weapons when it was winning the war, and urged U.S. President Barack Obama not to attack Syrian forces. REUTERS/Alexei Nikolskyi/RIA Novosti/Kremlin (RUSSIA - Tags: POLITICS HEADSHOT) ATTENTION EDITORS - THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: Reuters

Batun tattalin arziki ke kan gaba

Duk da haka dai taron na G20 ba zai zama wani dandali da zai karkata ga manufofin ketare ba, zai fi mayar da hankali ne kan batutuwan tattalin arziki, musamman wurin da aka kwana ga sauye-sauyen kasuwannin hada-hadar kudi, kamar yadda aka ji shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na fadi a wani sako ta bidiyo.

Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) redet am 03.09.2013 während der Sitzung des Bundestags in Berlin. Weniger als drei Wochen vor der Wahl ist der Bundestag zu seiner voraussichtlich letzten Sitzung zusammengekommen. Foto: Hannibal/dpa
Hoto: picture-alliance/dpa

"Da farko za a mayar da hankali kan tattalin arziki da kudi. Sai kuma batun ci-gaban kasashe. A taron G20 da ya gudana a Koriya ta Kudu shekaru uku da suka wuce mun amince da cewa kamata ya yi a ba wa kasashe matalauta wakilci a cikin shirye-shiryen G20 kuma tattalin arzikin duniya zai yi aiki ne idan aka samu ci-gaba a kasashe matalauta. Daga baya za mu tattauna game da manufofin ketare kuma a bana a kan batun Siriya."

Ci-gaba a kasuwannin kudi

Wasu shugabannin kasashe sun gamsu da sauye-sauyen da ake yi a kasuwannin kudi wanda aka kaddamar a taron kolin birnin London a shekarar 2009. Martin Faust na Kwalejin koyan hada-hadar kudi dake birnin Frankfurt a nan Jamus ya ce an samu nasarori.

"Ko shakka babu an yi hobasa. Yanzu bankuna sun samu karin jari na rigakafi. Sai dai har yanzu muna da matsala ta girman wasu bankunan fiye da kima, wadanda idan suka shiga matsala dole kasa ta kai musu dauki. A nan ina ganin da sauran aiki a gaba."

Sauran masana tattalin arziki na masu ra'ayin cewa ana kan turbar da ta dace sai dai da sauran rina a kaba. Kuma taron kolin na St. Petersburg na ranakun Alhamis da Juma'a, inda aka tsananta 'yancin gangami domin samar da kyakkyawan yanayin musayar yawu ba zai kai ga tattauna dukkan batutuwan na kudi da rage basussukan dake kan kasashe ba.

Mawallafa: Henrik Böhme / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu