1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Taron Cope 28 zai bai wa kasashe matalauta kudade

November 30, 2023

Kimanin kasashe 200 sun amince da a kafa asusun tallafa wa kasashen da matsalar dumamar yanayi ke yi wa lahani yanzu a duniya. Wannan ya fito ne daga taton sauyin yanyayi.

https://p.dw.com/p/4Zdpd

Kasashen dai da ake ganin za a taimaka musu, su ne kasashe matalauta a duniyar wadanda ke shan wahalar dumamar yanayin a halin da ake ciki.

Wannan dai mataki ne da ake yi wa kallon farawa da kafar dama a taron duniya kan sauyin yanayi da aka fara a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Shugaban taron mai lakabin Cope 28, Sultan Ahmed al-Jaber, wanda shi ne ministan masana'antu da ci gaban fasaha a Hadaddiyar Daular Larabawa, ya ce matakin sako ne da ke nuna nasarar wannan muhimmin taro na Dubai.

Kasashe da dama dai sun sanar da kudaden taimako da za su bayar, cikin har da Daular ta Larabawa da ta ce dala miliyan 100.

Burtaniya ta ce yi alkawarin bayar da dala miliyan 51 Amurka dala 17 da dubu 500 sai kuma Japan da ta yi alkawarin dala miliyan 10.