Taron Charm-El Cheick a game da rikicin yankin gabas ta tsakiya
June 24, 2007Talla
Gobe ne a birnin Charm El Cheik na ƙasar Masar, za a ganawar keke da keke tsakanin Praministan Isra´ila Ehud Olmert, da shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, da zumar farfaɗo da batun zaman lahia a yankin gabas ta tsakiya.
Wannan taro zai wakana mako guda bayan russa gwamnatin hadin kasa da Praministan Isma´il Hanniey ya jagoranta.
A jajibirin taron, gwamnatin Isra´ila ta bayyana balle takunkumin da ta kargamawa hukumar Palestinawa, domin tallafawa Mahamud abbas ya fuskanci tawayen kungiyar Hamas, wada a halin yanzu ke rike da zirin Gaza.
Ismail Hanniey ya bayyana adawa ga wannan mataki na mika kudaden ga Mahamud Abbas, a cewar sa kudi ne , wanda dukkan Palestinawa ba tare da banbanci ba, ta kamata su mora.