Taron AU kan tsaro da Ebola a Afirka
January 30, 2015Talla
Gabannin taron na yau dai, shugabar kungiyar ta AU Nkosazana Dlamini-Zuma ta yi kiran hada karfi a karfe wajen dakile aiyyukan masu kaifin kishin addini da ke cin karensu ba babbaka a wasu kasashen nahiyar.
Tuni dai kwamitin tsaro da zaman lafiya na AU din ya bukaci a samar da wata rundunar soji mai yawan dakaru dubu 7 da dari 5 domin kawo karshen tada kayar bayan 'yan bindiga.