1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Afrika da Indiya

Yusuf IdrisApril 8, 2008

A yau ne aka buɗe taron yini biyu tsakanin India da wasu ƙasashen Afrika

https://p.dw.com/p/DeSp
Primiyan India, Manmohan Singh.Hoto: AP Photo

A yayin da India ta buɗe taron ta na kwanaki biyu da ƙasashen Afrika ke halarta a Birnin New Delhi ranar wannan talata,alamu na nuna cewa ƙasashen na Afrika zasu dara,idan aka yi la'akari da batutuwan da suka mamaye wurin taron.

A jawabinsa na buɗe taron ,Prime ministan ƙasar India,Manmohan Singh,ya sanar da yin da sassauci akan harajin fitar da kaya,wanda a cewarsa,zai amfani ƙasashen Afrika 34,

"Yace,lokaci yayi da za a samarda sabuwar hanya mafi dacewa ta aiki tare a wannan ƙarni na 21.Da haɗin kai,kimanin Al'ummomin India billion biyu da Na Nahiyar Afrika,zasu kafa tubali mai inganci wanda zai zame abun koyi a duniyar ƙasashe masu tasowa"

Prime Ministan ya ce ƙasar Indiya zata haɗa gwiwa da ƙasashen Afrika wajen haɓaka harkar noma,kayayyakin more rayuwa,ilmi da kananan masana'antu tare da fasahar sadarwa,sannan yace za a bada kusan dala miliyan ɗari biyar a matsayin taimako na gudanar da ayyuka,

"Manufar mu ce,mu kara irin tallafi da muke bawa Afrika ta fannin kasafin mu na ma'aikatar kula da harkokin waje ,waɗanda za a iya amfani dasu wajen gudanar ayyukan raya cigaban waɗannan ƙasashe.Cikin shekaru 5 zuwa 6 masu gabatowa ,muna da niyyan gudanar da ayyuka na raya ƙasashen ,da ƙarin kimanin dala million 500"

Prime Minista Manmohan Singh dai yayi suna wajen nuna goyon baya akan gwagwarmayar ƙasashen Afrika na yaƙi da mulkin mallaka,abin da ya jawo mai farin jini a Nahiyar.

Sai dai masu nazari akan al'amura sun ce ƙasar ta India ta fara samun rashin goyon bayan ƙasashen Afrika ne bayan ta kaikaita akalar kasuwancin ta zuwa ƙasashen Amurka da nahiyar turai bayan kuwa ƙasashen China da Japan sun yi nisa da harkokin kasuwanci da ƙasashen Afrika.

Shugaban ƙasar jamhuriyyar Demokraɗiyyar Kongo Joseph Kabila, wanda ya halarci taron,yace Dangantaka tsakanin ƙasashen Afrika da wasu ƙasashe bata wuce batun baki kawai,ya kara da cewa Maganganu da jawabai da sun kasance maganganu kawai shekara da shekaru,inda yace ana bukatar ganin ayyuka na zahiri.

Shi kuwa Shugaban ƙungiyar ƙasashen Afirka AU, Alpha Umar Konare,ya ce ƙasashen Afrika na bukatar taimakon ƙasar India ne ta ɓangarorin Ilimi,kiwon Lafiya da kimiyya.Sannan ya ce dole ne ƙasar India ta buɗe kunuwanta akan bukace-bukacen jama'ar ƙasashen Afrika,kuma ya bukaci Afrika da ta dai na zama kasuwar da kowa zai zo ya ɗibi abin da yake so ba tare da ta amfana da wata riba ba.

Shima shugaban ƙasar Uganda,Yoweri Museveni, yace duk da cewa ƙasashen Afrika sun sami 'yancin kai ne kusan lokaci guda,tattalin arzikin ƙasashen Asia ya fi na takwarorinsu na Afirka ne saboda sun keɓe kansu,kamar yadda suma ƙasashen Afrika suka yi,sai dai yace yanzu an gyara waɗannan manufofin.

Za a dai kammala taron na kwanaki biyu ne,wanda ƙasashen Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo,Najeriya,Afrika ta Kudu da wasu ƙasashen ke halarta, ranar Laraba.