1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙungiyar tsaro ta NATO da Tarayyar Turai akan Libya

March 10, 2011

Mahawara na cigaba da gudana tsakanin NATO da Eu a birnin Brussels, adaidai lokacin da Jamus ta sanar da dakatar da ƙuɗaɗen Libya dake Bankunanta

https://p.dw.com/p/10X0M
Jami'ar kula da ketaren EU Catherine AshtonHoto: AP

Ƙungiyar tsaro ta NATO da Tarayyar Turai na tattaunwa akan halin da ake ciki a Libya, adaidai lokacin da ƙazamin faɗa ke cigaba da gudana tsakanin 'yan adawa da magoya bayan shugaba Moammer Gaddafi. Gabannin buɗe taron ɓangarorin biyu dai, babban Sakataren NATO Anders Fogh Rasmussen ya ce har yanzu gamayar dakarun tsaron na nazarin matakin sojin da za su ɗauka.

A cewarsa hakika NATO ba ta neman hanyar shiga rikicin Libya. Sai dai  Dakarunsu za su ci gaban da kasancewa cikin shiri, amma ba matakan aiwatar da komai tukuna.

Rahotanni daga Libya na nuni da cewar Dakarun Gwamnati sun cimma nasara a sassa daban-daban ciki har da Garuruwan Ras Lanuf, Bin Jawad da Zawiyah.

A halin da ake ciki yanzu haka dai, Jamus ta dakatar da asusun kuɗaɗen ajiyar  babban Bankin da wasu kuɗaɗen Libyan dake nan tarayyar Jamus. Ma'aikatar harkokin tattali ta shaidar da cewar wannan mataki da aka ɗauka ya shafi Asusu guda 193 dake Bankunan Jamus 14, ciki har da babban Bankin Jamus da kimanin kuɗi sama da Euro biliyan 50.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar Edita: Umaru Aliyu