Taron ƙungiyar ƙasashen Larabawa game da Siriya
July 3, 2012Kungiyar haɗin kan ƙasashen larabawa tare da haɗin gwiwar gamayyar ƙasa da ƙasa, ta shirya zaman taro a birnin Alƙahira na ƙasar Masar, domin tattana rikicin ƙasar Siriya.
A jawabin da ya gabatar, Sakatare Janar na ƙungiyar ƙasashen Larabawa Nabil El Araby, ya yi kira da babbar murya ga 'yan adawar ƙasar Siriya su haɗa kai domin fuskantar dakarun shugaba Bashar Al-Assad.
An dai samun rabuwa kanu mai ƙarfi tsakanin ƙungiyoyi daban-daban masu adawa da gwamnatin Siriya, inda wasu daga cikinsu su ka ƙauracewa taron.
Itama Komishinar kare haƙƙoƙin bani Adama ta Majalisar ɗinkin Duniya Navi Pillay, ta zargin gwamnati da 'yan adawar Siriya da hallaka fara hulla.Daga farkon wannan rikici zuwa yanzu, Majalisar Dinkin Duniya ta ƙiyasta mutane fiye da dubu 16 da suka rasa rayuka a cikin wannan rikici.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu