1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro tsakanin Merkel da Sarkozy

December 10, 2010

Jamus da Faransa sun nuna adawa da tsarin asusun ceto tattalin arzikin ƙasashen EU.

https://p.dw.com/p/QVgS
Angela Merkel ta Jamus da Nicolas Sarkozy na FaransaHoto: AP

Tarayyar Jamus da kuma Ƙasar Faransa sun sa ƙafa sun yi fatali da shawarar da aka bayar na girka wani sabon tsari da zai ceto ƙasashen Turai da ke cikin mawuyacin halin tattalin arziki. Wannan mataki na su ya zo ne mako ɗaya kafin gudanar da taron ƙoli na ƙasashen da ke amafni da Euro domin duba yadda za a aiwatar da assussun ƙasashen Turai da zai ƙunshi miliyon dubu 750 na Euro.

 A lokacin wani taron haɗin gwiwa da suka gudanar a birnin Fribourg na Jamus da ke kan iyakokin ƙasashen biyu, Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa da kuma shugabar gwamnatin Jamus wato Angela Merkel  sun ce bai kamata a aiwatar da shirin  da aka ƙirƙiro da shi ba, bayan da ƙasar Girka ta fuskanci koma bayan tattalin arziki. Shugabannin suka ce a shirye suke su bayar da hadin kan da ake bukata domin ɗaukaka darajar takardar Euro a duniya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal 

Edita: Abdullahi Tanko Bala