1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Mohammad Mursi shugaban ƙasar Masar

July 2, 2012

Mohammad Mursi mai shekaru 61 a duniya ya zama shugaban ƙasar Masar fara hula na farko tun bayan samun 'yancin kan ƙasar.

https://p.dw.com/p/15Ptf
25/06/12 11:42:24 1929x2800(446kb) Muslim Brotherhood's president-elect Mohamed Morsy speaks during his first televised address to the nation in Cairo Muslim Brotherhood's president-elect Mohamed Morsy speaks during his first televised address to the nation at the Egyptian Television headquarters in Cairo June 24, 2012. Morsy's victory in Egypt's presidential election takes the Muslim Brotherhood's long power struggle with the military into a new round that will be fought inside the institutions of state themselves and may force new compromises on the Islamists. Picture taken June 24, 2012. To match Analysis EGYPT-ELECTION/STRUGGLE/ REUTERS/Stringer (EGYPT - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

Mohamed Mursi, saban shugaban ƙasar Masar a ƙarƙashin tutar jam' iyar 'yan uwa musulmi an aihe shi a watan Ogusta na shekara 1951, wato yanzu kenan idan muka lissafa ya na da shekaru 61 a duniya.An aihe shi a jihar Ach-Charkiya kuma anan ne ya yi karatunsa na firamari.Iyayensa talakawa ne kuma manoma, saboda haka bai tasa cikin wani yanayi na jin ɗaɗi sosai ba.

Bayan ya gama firamari da sakandari ya shiga jami` ar birnin Alkahira inda ya yi karatu ta fannin ilimi gine-gine.

A jam'iyar ta birnin Alƙahira ne ya shiga ƙungiyar 'yan uwa musulmi.

Tsakanin shekara 1978 zuwa 1995, ya yi karatu a ƙasar Amurika.

Bayan ya dawo gida Masar, ya samu wani matsayi a sashen da ke kula da gine-gine na jami'ar Zagazig ta ƙasar Masar.

Dabra da haka ya na riƙe da muƙamai daban-daban a ƙungiyar 'yan uwa musulmi, yayi zama mai kula da hulɗa da ƙasar Sudan, sannan ya riƙe muƙamin sakatare mai kula da hulɗa da ƙasashen ƙetare, kamin daga bisani ya zama memba a komitin ƙoli na wannan ƙungiya.Sannu a hankali dai ya zama mai ƙarfin faɗa aji a ƙungiyar 'yan uwa musulmi.

A zaɓen 'yan majalisar dokoki da aka shirya a ƙasar Masar a shekara 2010, shi ya zama daraktan yaƙin neman zaɓe na ƙungiyar 'yan uwa musulmi.Sakamakon zaɓen ya nunar da cewar, ƙungiyar ta samu rinjaye amma gwamnatin shugaban Hosni Mubarak ta yi aringinzon ƙuri`u.

Bayan juyin juya halin da aka kifar da shuga Mubarak a shekara da ta gabata,sai ƙungiyar 'yan uwa musulmi ta rikiɗa zuwa jam'iyar siyasa da aka raɗawa suna jam'iyar 'yanci da adalci awatan Afrilu na shekara 2011,kuma magoya bayan wannan jam'iya su danka shugabancin ta ga Mohamed Morsi.

Egypt's new President Mohamed Mursi (R) listens to the national anthem before speaking at Cairo University June 30, 2012. Mursi said on Saturday the military that took charge when Hosni Mubarak was overthrown last year had kept its promise to hand over power, speaking at a ceremony to mark the formal transfer of authority. REUTERS/Egyptian Presidency/Handout (EGYPT - Tags: POLITICS ELECTIONS) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: Reuters

Kamar dai abinda hausawa ke cewa ne rabo rabbabe wai tsuntsu daga sama gassashe, domin ita jam'iyar PLJ a lokacin da ta tatance ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasa, ta bada sunan Khairat al-Chater, to amma sai kotin tsarin mulki ta yi watsi da sunan shi, tare da hujjar cewar an sha tsare shi kurkuku a zamanin Mubarack.

Saboda hake don kar jam'iyar ta kasance ba ta da ɗan takara sai ta bada sunan Mohamed Morsi, domin ya maye gurbin Khairat al-Chater , ka ji yadda a ka yi har ya zama dantakara jam'iyar 'yan uwa musulmi kuma yayi nasara kai wa ga zagaye na biyu inda zai fafatawa da ɗan takara Ahmed Shafik tsofan firaminsitan Hosni Mubarak wanda magoya bayan 'yan uwa musulmi da matasan da suka ƙaddamar da juyin juya hali suke tunanin cewar idan har Ahmed Shafik ya yi nasara zaman shugaban Masar to tamkar za a komawa ne gidan jiya noman goje.

To a ƙarshe dai bayan tsawan mako guda na jira sakamakon Hukumar zaɓe ranar Lahadin da ta wuce ta bayyana Dr.Muhamad Mursi a matsayin a matsayin ɗan takara da ya lashe zaɓen da kashi kusan 52 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa kuma shine fara hula na farko da ya taɓa hawa wannan matsayi tun lokacin da Masar ta samu 'yancin kanta.

ƙalubalen da ke gaban Mohammad Mursi

Babban ƙaluble shine wace irin ma'amala zai yi da sojoji wanda kwanaki kaɗan kamin bayana sakamakon zaɓe suka ɗauke wasu sassa na mulki daga fadar shugaban ƙasa hasali ma abinda ya shafi tsaro na ciki da na iyakokin ƙasa,da harakokin kuɗi.Kenan shugaban da ba shi da soja da 'yan sanda da kuma assun gwamnati a na iya danganta shi da abinda hausawan Nijar ke cema 52 soji ba bindiga.

Egypt's new President Mohamed Mursi (C) and Field Marshal Mohamed Tantawi (5th L), head of Egypt's ruling Supreme Council of the Armed Forces (SCAF), pose for a picture during a ceremony where the military handed over power to Mursi at a military base in Hikstep, east of Cairo, June 30, 2012. Mursi was sworn in on Saturday as Egypt's first Islamist, civilian and freely elected president, reaping the fruits of last year's revolt against Hosni Mubarak, although the military remains determined to call the shots. The military council that took over after Mubarak's overthrow on February 11, 2011, formally handed power to Mursi later in an elaborate ceremony at the desert army base outside Cairo. REUTERS/Mohamed Abd El Moaty/Egyptian Presidency/Handout (EGYPT - Tags: POLITICS ELECTIONS MILITARY) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: Reuters

Sannan wani ƙalubalen shine saje haɗe kan kasa, a game da haka a cikin jawabin farko da yayi Mohamad Mursi ya ɗauki alƙawarin gudanar ada jagoranci ba tare da nuna wariyar addini ko ta jinsi ko ta siyasa ba.

A ɗaya wajen game da harkokin diplomasiya a nan ma akwai namijin aiki, domin ƙasashen Turai da Amurika lalae sun yi lale marhabin da Mursi kuma sunyi alƙawarin yin aiki da shi to amma akwai abin hausawa ke cewa ta ciki na ciki, mussamman game da kalamomin da aka ce an jiyo daga bakinsa, inda ya ce zai ƙarfafa dangantaka da Iran, kuma ka san wannan ƙasashe tsakaninsu da Iran ana cikin zaman doya da manya ja.Yanzu abinda jama'a ta zura ido ta gani shine ko saban shugaban zai cika wannan alƙawura da ya ɗauka, da ma alƙawarin da yayi na ci gaba da muntunta yarjejeniyar zaman lafiya da Masar ta cimma da Isra'ila a shekara 1975.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal