1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Manchester United

June 25, 2011

Ƙungiyar ƙwallon ƙafar Manchester United ta Birtaniya ta yi shekaru 133 da girkuwa.

https://p.dw.com/p/11jUl
Manchester United Logo

Ƙungiyar ƙwallon ƙafar Birtaniya ta Manchester United an girka ta tun shekara 1878 wato yanzu shekaru 133 kenan a wani gari mai suna Trafford kusa da birnin Manchester.

Da farko sunan kungiyar Newton Heath, wato suna wani mutumen ne da ya ke daga mutanen da su ka kirkiro gasar cin kofin kwallon kafa  Birtaniya a shekara 1882.

Sai a shekara 1902 ne, shekaru kusan 100 kenan da su ka wuce aka cenza suna daga Newton Heath zuwa Manchester United.

Ƙungiyar ta fara cin kofin ƙwallon Birtaniya na ƙasa a shekara 1909 inda ta yi bugun ƙarshe da Bristol City ci ɗaya da nema.

Daga shekara 1920 zuwa 1930 Manchester United ta fuskanci matsaloli masu yawa wanda dalilin su aka maido ta rukunin ƙungiyoyin ƙwallo na mataki na biyu.

Sai su ka samu wani hamshaƙin mai kuɗi mai suna James Gibson shi ya biya duk bassusukan da a ka tambayo ƙungiyar,a lokacin ta  kutsa cirin tsara har ta yi nasara komawa sahun ƙungiyon masu wasa a mataki na farko.

Amma a shekara 1958 Manchester United ta shiga wani mawuyacin halin sakamakon haɗarin jirgin sama a birnin Munich na Jamus inda fittatun yan wasanta shida suka rasa rayuka.

A faɗin duniya kaf!, Manchester United itace ƙungiyar ƙwallon kafar da ta fi samun yawan kofi.

Luis Nani Fußballspieler Manchester United
Hoto: picture-alliance/empics

A jimilce ta ci kofi ɗaya na bi daya har kofuna fiye da 60, sannan ta samu tutar ƙungiya mafi tasiri har sau 60 shima.

Kan kofuna na Champions Leagues kann kofuna na gasa tsakanin kasashen turai, ko kuma na duniya gaba daya.

 A fannin gasar cikin gida Birtaniya ta ci kofi har sau 19, sai kuma a wasanni na hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar turai inda ta ci kofi har sau takwas.

A lokacin da shugaban ƙungiyar  mai ci yanzu Sir Alex Ferguson ya fara jogarancin Manchester United a wannan lokacin kungiyar ta kara bunkasa kuma ta kara samun tasiri da magoya baya.Tun daga 1986 Ferguson ke shugabancin Manchester United

Yan wasan da suka haskaka tarmamuwar Manchester United su na da yawa ba za mu iya zana su ba.

David Beckham Porträt WM 2006
Hoto: picture-alliance / dpa

To amma wasu daga ciki wanda ma´abuta ƙwallon ƙafa su ka fi shawa, sun hada da Erik Kantona, wanda tsawan shekaru ukku ya buga wasa a Manchester wato dag 1992 zuwa 1995.

Akwai David Bekham, Christiano Ronaldo, Rio Ferdinand,Roy Keane, Paul Scholes,Ryan Giggs da dai sauran su.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu