1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarayyar Turai ta dakatar da horon soja a Mali

May 17, 2022

Kungiyar Tarayyar Turai, ta nuna rashin jin dadinta da matakin Mali na ficewa daga kungiyar G5 Sahel. Kungiyar ta ce ta dakatar da bai wa sojojin kasar horo na wani lokaci.

https://p.dw.com/p/4BRH1
Militär I Mali I UN-Truppr EUTM
Hoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/MAXPPP/dpa/picture alliance

Babban jami'in da ke kula da harkokin ketare na Kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell, ya ce kungiyar za ta dakatar da horon da take bai wa sojoji na wucin gadi a kasar Mali. 

Bayan ganawar da ya yi ministocin tsaron kungiyar a Brussels babban birnin kasar Beljiyam, Mr. Borrell ya ce duk da takaicin da suka ji da matakin Mali na ficewa daga kungiyar G5 Sahel, ba za su dakatar da aikin horon ba kwata-kwata ba.

A ranar Lahadin da ta gabata ce dai kasar Mali ta sanar da aniyarta ta ficewa daga kungiyar G5 Sahel da ma rundunar kawancen yaki da ta'addanci a yammacin Afirka da ke samun tallafin kasashen na Turai.

Babban jami'in na kungiyar EU, ya kuma kalubalanci matakin majalisar mulkin soji a Mali na kin raba gari da sojojin haya na kamfanin Wagner daga kasar Rasha da ake zargin su da take hakkin bil Adama. 

An dai kafa kungiyar ta G5 Sahel mai kunshe ne da dakarun kasahen Nijar da Chadi da Burkina Faso da kuma Mauritania a shekarar 2017 da nufin yaki da mayaka masu ikrarin jihadi a yankin.