1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tanzaniya ta janye kudin bikin ranar 'yancin kai

December 6, 2022

Tun da farko dai an tsara kashe kudade Dala 445,000, kudin da a yanzu aka mayar da su wajen gina dakunan kwanan dalibai guda takwas a wasu makarantun furamare da ke kasar.

https://p.dw.com/p/4KXxe
Hoto: Hannah Mckay/AFP/Getty Images

Shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta soke bikin ranar tunawa da 'yancin kan kasar da aka tsara gudanarwa a ranar Jumma'a, ta kuma umurci a yi amfani da kudaden da aka ware wa bikin wajen gina dakunan kwana ga dalibai masu bukata ta musamman a kasar.

Gwamnatin ta Tanzaniya ta ce tuni ta fitar da kudaden domin a fara aikin, ta kuma fito da wasu hanyoyin da za a yi bikin tunawa da samun 'yancin kan kasar karo na 61 ba tare da an kashe kudi daga lalitar gwamnati ba.