1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama madugun adawar Tanzaniya

July 21, 2021

A Tanzaniya rahotannin da ke fitowa daga bangaren adawar kasar, na nuni da cewa an kama madugun adawar kasar tare da wasu kusoshin jam'iyar 10.

https://p.dw.com/p/3xnUN
Freeman Mbowe Oppositonsführer Tansania
Hoto: DW/E. Boniphace

'Yan adawar kasar ta Tanzaniya dai, na ganin hakan a matsayin wata kutungwilar siyasa da shugabar kasar Samia Suluhu take daurawa daga inda tsohon shugaba marigayi John Magufuli ya tsaya. Jami'iyyar adawar kasar dai ta ce an kama shugabanta Freeman Mbowe ne da sauran jiga-jigan jam'iyyar, yayin da suke kokarin shirya gudanar da wani taro a wannan Laraaba domin tattaunawa kan sabon kundin tsarin mulkin Tanzaniyan.

Sai dai kuma wasu na ganin cewa kamen ya biyo bayan umarnin da gwamnatin kasar ta sanya ne na haramta gudanar da taro ba tare da izinin gwamnati ba, a wani mataki da gwamnatin Shugaba Samia ta dauka na takaita yaduwar annobar corona. Sai dai kuma 'yan adawa a kasar na ganin hakan tamkar take hakkin dan Adam ne.