1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafin Euro million 4 daga turai zuwa Bakassi

Zainab A MohammadOctober 28, 2005
https://p.dw.com/p/BvSb

Hukumar gudanarwa na kungiyar gayyar turai ta bada tallafin dala million 4 da dubu dari 8,kwatankwacin Euro million 4 domin ginin kann iyakokin kasashen Nigerias da Kamerou.

Sanarwar data fito daga ofishin hukumar gudanarwa na kungiyar gamayyar turan na nuni dacewa wannan tallafi nada matukar muhimmanci wajen aiwatar da hukuncin da kotun kasa da kasa ta yanke akan iyakar kasashen biyu a shekarata 2002.

Kazalika zai kuma taimaka matuka gaya wajen warware takaddamar kann iyaka da bangarorin biyu suka jima suna takun saka da juna akansa.

Daga cikin adadin kudindai,zaa ajiye dala million3.95 cikin asusun majalisar dunkin duniya ,ayayinda euro dubu 50 zaayi amfani dasu wajen tsara kann iyaka da yadda aikin zai gudana.

Gwamnatocin Nigeria da Kamarou sun bada tallafi na karin dala million 3 kowannensu,

Hakkin zartar da wannan akki baki daya dai ya rataya ne a wuyan komitin hadin gwiwan kasashen Ni9geria da kamaru,wadanda mambobinta suka hadar da wakilan kasashen biyu,da majalisar dunkin duniya ,akarkashin jagorancin jakadan mdd na musamman Ahmedou Ould Abdallah.

Akwai kuma tawagar jamian fasaha,da suka hadar da kwararru ta fannin tsara gine gine daga kasashen biyu da kuma mdd,wadanda kuma a farkon wata mai kamawa zasu bayyana akan iyakokin ,domin fara aiki.

A shekarata 2003,hukumar turan ta bada tallafin Euro dubu 400,domin aiwatar da rukuni na farkon yanka kann iyakan,wanda kuma ke zama zakaran gwajin dafin yadda ainihin tasiwirar aikin zai kasance.

Kasashen Nigeria da Kamaru dai sun jima suna fama da rikici kann tsibirin Bakassi ,yankin dake gabar guinea,kuma ke dauke da albarkatun mai da kifi,fiye da shekaru 10 da suka gabata.Sakamakon wannan rikicin mallakan tsibirin bakasin tsakanin kasashen biyu dai,an yi asaran rayuka masu yawan gaske.

A shekarata 2003 nedai,kotun sauraron karararraki na kasa da kasa dake birnin Hague,ya shiga tsakani tare da yanke hukuncin bawa kamarun yankin na bakassi.

A tsakiyar watan Oktoba bangarorin biyu sun amince da gabatar shirin yarjejeniya a dangane da janye dakarun nigeria daga Bakasin,yarjejeniyar da zaa mikawa shugabannin kasashen biyu da sakatare general na mdd.

A karkashin tsohuwar yarjejeniyar wadda mdd ta amince dashi,ya kamata Nigeria ta janye dakarun daga yankin takaddaman a watan Satumba,amma hakan bata kasance ba,inda ta bukaci a bata karin lokaci.