1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafi ga 'yan gudun hijirar Somaliya

July 17, 2011

Majalisar Dinkin Duniya ta fara aika agajin gaggawa a matsugunnan 'yan gudun hijirar da ke fama da yinwa a yankin gabacin Afirka

https://p.dw.com/p/11x5u
Hoto: picture alliance / dpa

Majalisar Dinkin Duniya ta kai agajin farko ga dubunan yan gudun hijira daga kasashen yankin kafan Afirka dake fama da bila´in yinwa.A cewar kakakin kungiyar UNICEF da ke Somaliya an kai agajin a Baidoa tare da amincewar kungiyar Shebab dake rike da wannan yanki.

A wata ziyasar da su ka kai a sansanin yan gudun hijira da ke Dadaab a kasar Kenya, shugaban Unicef da Sakataran bada taimakon raya kasa na Birtaniya, sun yi kira ga kasashe masu hannu da shuni, su kara himmantuwa domin ceton al´umomin sansanin dake cikin matsanancin kuncin rayuwa.Kusan mutane dubu 400 ke raye a wannan sansani ,kuma mafi yawan su sun hito daga kasar Somaliya.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Zainab Mohammed Abubakar

A jimilce mutane miliyan goma ne,wanda suka hada da kananan yara miliyan biyu a ka kiyasta cewar suna fama da matsanciyar yinwa a yankin kafan Afrika.

Shugabar gwamnmatin Jamus Angela Merkel, ta alkawarta taimako cikin gaggawa na euro miliyan goma.