1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafi ga matalautan kasashe ya ja hankali a taron sauyin yanayi

December 13, 2014

Kasashe masu karfin tattalin arziki na jaddada karkata kan rage yawan iskar Carbon da danginta da ke gurbata muhalli sai dai suna nokewa wajen batun sakin kudade.

https://p.dw.com/p/1E3md
Lima - COP 20
Hoto: Reuters/E. Castro-Mendivil

Tattaunawar taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin Lima na Peru ta tsallake wa'adin da aka tsara mata tun da fari ya zuwa ranar Asabar inda masu tattaunawar suka ce matsalolin da kwararrun kan muhalli suka gabatar sun gaza bayyana irin alhakin da ya rataya a wuyan kowace kasa da za ta amince da shi a taron da za a yi birnin Paris na kasar Faransa a shekara mai zuwa.

Taron na makwanni biyu da ya samu wakilai daga kasashe fiye da 190 an shirya kammala shi a ranar Juma'a ko da yake irin wannan taro da ake shekara-shekara ba kasafai ake kammala shi a lokacin da aka tsara ba.

Daya daga cikin batutuwan da suka zama kadangaren bakin tulu na zama fayyace alkawuran da kasashen za su dauka dan gabatar da shirin yarjejeniyar da ake son kullawa a birnin Paris.

Kasashe masu karfin tattalin arziki na jaddada cewa hankali ya karkata kan yawan isakar Carbon da ake fitarwa da sauran nau'oin iskar gas da ke gurbata muhalli sai dai suna nokewa wajen shigar da batun sakin kudade da za a yi amfani da su wajen tallafa wa kasashe matalauta domin rage zafin illar ta sauyin yanayi, wanda cibiyar kula da muhallai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce a makon da ya wuce, aikin zai lashe Dala miliyan dubu 200 nan da shekara ta 2050.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo