1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Afghanistan ya rincabe

Ramatu Garba Baba
August 13, 2021

Rundunar kawance da Amirka ta jagoranta a yaki da Taliban, ta kawar da batun tura duk wata runduna don taimaka wa gwamnatin Afghanistan murkushe kungiyar da ke son karbe mulki.

https://p.dw.com/p/3yxEM
Afghanistan Update Bildergalerie Taliban Kämpfer Kandahar
Hoto: AFP via Getty Images

Kungiyar tsaro ta NATO ta gudanar da wani taro na gaggawa kan fadan da ake a Afghanistan, taron da na wannan Juma'ar, ya mayar da hankali kan shirin tura runduna ta musanman, domin kwashe ma'aikatan ofishin jakadanci na mambobin kungiyar da ke aiki a Kabul da rikicin ya rutsa da su.

A yanzu, babu batun taimaka wa kasar a fadan da take da Taliban, kamar yadda Shugaba Joe Biden na Amirka ya fadi, sai dai a wata tattaunawa da DW, Egon Ramms, wani tsohon janar na rundunar sojan kasar Jamus da ya jagoranci yaki da Taliban, ya ce, akwai gazawa a bangaren rundunar gwamnatin Afghanistan da kuma kuskure da bangaren rundunar kawance da Amirka ta jagoranta ta tafka idan aka duba matakin janye rundunar kawance daga cikin kasar. Ya ce, ''Da makamai da horon da suka samu daga rundunar sojin Amirka da Jamus a shekarun da suka gabata, bai dace su yi sake ba, har Taliban ta yi kokarin kwace mulki daga hannun gwamnati, ganin nasarorin da kungiyar ke samu a yanzu, ina ganin, kuskuren da muka yi a can baya, shi ake kokarin maimaitawa''

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa, mayakan Kungiyar Taliban sun kwace iko da garin Kandahar birni na biyu mafi girma da kuma gundumar Logar, mai tazarar kilomita hamsin daga Kabul, babban birnin kasar. Masana na ganin, idan har ba a gaggauta daukar matakin dakatar da fadan ba, to nan bada jimawa Taliban za ta karbe ikon shugabancin kasar ta Afghanistan.