1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ta haramtawa jami'in MDD shiga Afghanistan

August 22, 2024

Gwamnatin Taliban a Afghanistan, ta haramta wa babban mai bincike kan hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan, Richard Bennett daga shiga cikin kasar.

https://p.dw.com/p/4jlSs
Babban mai bincike na mussaman kan hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan, Richard Bennett
Babban mai bincike na mussaman kan hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan, Richard Bennett Hoto: Ebrahim Noroozi/AP Photo/picture alliance

Kakakin gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahida ya zargi Bennett da yada wasu manufofi da ba su gane musu ba a cikin Afghanistan. A cikin sanarwar da ya fitar, Bennett ya bukaci gwamnatin Taliban ta janye matakin nata, kana ya ce zai ci gaba da gudanar da aikinsa daga wajen kasar. A baya-bayan nan ne dai, Bennett ya ce yadda Taliban ke tafiyar da rayuwar mata da 'yan mata a kasar laifi ne na cin zarafin bil Adama.

Tun dai a shekarar 2022, Majalisar Dinkin Duniya ta nada Benett a matsayin babban mai binciken, shekara guda bayan da Taliban ta sake kwace ragamar mulkin kasar.