1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gina gida ga Kashim Shettima

December 4, 2023

A yayin da ake ci gaba da kukan karancin a kudi, miliyoyin al'ummar Najeriya na mai da martani kan wani sabon shirin gina dankareren gida ga mataimakin shugaban kasar.

https://p.dw.com/p/4ZmDk
Najeriya | Mataimakin Shugaban Kasa | Kashim Shettima
Tsohon gwamnan jihar Borno kana mataimakin shugaban Najeriya, Kashim ShettimaHoto: Reuters/A. Sotunde

Duk da cewar dai tun a shekara ta 2010 ne gwamnatin Najeriyar ta amince da ginin sabon gida ga mataimakin shugaban kasa, sai a shekarar da ke shirin kamawa ne dai masu mulkin kasar suka ce suna shirin fara shi. Akalla Naira miliyan dubu 15 ne dai Ma'aikatar Babban Birnin Tarayyar ta Abuja ta ce ana da bukata, domin ginin gidan na alfarmar son kowa. Tuni dai ma'aikatar ta gabatar da wannan bukata tata a gaban majalisun kasar guda biyu, bukatun kuma da ya zuwa yanzu ke jawo kace-nace cikin kasar da ke karatun matsatsi. Honourable Hassan Shehu Hussain dai na zaman dan majalisar wakilai na kasar daga jihar Kano, kuma ya ce ba ya shirin goyon bayan sabuwar bukatar ta 'yan mulkin. Duk da tsadar rayuwa da hauhawar farashi dai, ana kallon yawan kudin ya wuce kima a Najeriyar da ke linkaya a kogin bashi.

Najeriya | Borno | Maiduguri | gudun Hijira | Rashin Tsaro | Boko Haram
A jiharsa ta Borno dai, dubban mutane na sansanin 'yan gudun hijira saboda rashin tsaroHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Mohammed Ibrahim na sana'ar ginin gidaje a kasar, kuma ya ce yawan kudin yana iya samar da gidaje kusan 600. Tuni dai matakin da ke jiran kallon tsaf a bangaren 'yan doka, ya fara janwo cece-kuce a bangaren kungiyoyi da masu rajin neman gyara kasar. Dakta Isa Abdullahi dai na sharhi kan tattalin arziki, kuma ya ce tunanin mahukuntan ya saba da halin da kasar ke ciki na matsatsi. Bambancin da ke tsakanin baki da zuciya ko kuma kokarin inganta rayuwar 'yan mulki, kusan kaso 45 cikin 100 na daukacin kasafin kudin shekarar badi dai na zaman kudin ruwa a kasar da ke dada cin bashi da nufin rayuwa. Mahdi Shehu dai yana sharhi ga kokarin inganta rayuwa, kuma ya ce yawan kudin yana iya sauya rayuwar da dama cikin kasar. Ko a shekarar da ke shirin shudewa dai an ware Naira miliyan dubu biyu da miliyan 500, domin yi wa gidan mataimakin shugaban kasar kwaskwarima.