1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takunkumin haramcin shawagin jiragen saman yaƙi a samaniyar Libiya

March 18, 2011

Bayan ɗariɗari da yayi a yanzu kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kafa dokar haramta shawagin jiragen saman yaƙi a samaniyar Libiya

https://p.dw.com/p/10cM6
Zaman taron kwamitin sulhu akan LibiyaHoto: picture alliance/dpa

A haƙiƙa sai bayan da tura ta kai bango ne kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da shawarar ƙaƙaba wa Libiya takunkumin hamarta shawagin jiragen saman yaƙinta a samaniyar ƙasar domin kare lafiyar al'umarta, musamman ma 'yan tawayen da suka yi wa Gaddafi huruji a gabacin Libiyar, waɗanda ke dab da fuskantar lugudan wuta ta sama daga jiragen saman yaƙin Gaddafi. Bisa ga alamu kuwa ƙudurin na kwamitin sulhu ya fara nuna tasirinsa na dakatar da hare-haren sojojin Gaddafi, inda ministan harkokin wajen Libiyan ya ba da sanarwar tsagaita wuta. To sai dai kuma ba tabbas game da abin da zai biyo baya.

Jamus ta yi rowar ƙuri'a

Jamus, daidai da ƙasashen China da Rasha sun yi rowar ƙuri'unsu a zauren kwamitin sulhun. Akwai kuma ƙwaƙƙwaran dalili game da haka. Domin kuwa tilas ne a yi taka tsantsan game da katsalandan soja a ƙasar. Haramta shawagin jiragen saman yaƙin abu ne da ake fatan zai taimaka a shawo kan Gaddafi ya shiga tattaunawa akan tsagaita wuta. To sai dai kuma murna na iya komawa ciki game da wannan fata da aka yi kuma ya zama wajibi Majalisar Ɗinkin Duniyar ta gabatar da wani sabon ƙuduri akan ɗaukar matakai na soja, in kuwa ba haka ba wannan barazanar ba ta da amfani. Ƙasashen Faransa da Birtaniya da kuma Amirka dai a shirye suke su yi katsalandan soja a yayinda sauran ɗaiɗaikun ƙasashen ƙungiyar tsaro ta NATO zasu ba da gudummawar kayan aiki.

Akwai ayar tambaya game da shiga yaƙi na dogon lokaci

DOSSIER Bild Dossierbild Libyen Luftangriff 3
Rikicin Libiya ka iya ɗaukar wani fasali dabamHoto: picture alliance / dpa

Amma kuma ayar tambaya ita ce ko wace ce daga cikin ƙasashen dake goyan bayan katsalandan soja ke da shirin shiga wani yaƙi mai ɗorewa a arewacin Afirka? Ƙasar Faransa ta janye daga takunkumin haramcin shawagin jiragen saman Iraƙi don kare Ƙurdawa a shekarun 1990. A can Amirka kuma, hatta a tsakanin sojojin ƙasar, akwai masu nuna gajiya da gundura da yaƙe-yaƙe, musamman ma ganin irin darussan da suka koya daga shisshigin soja a ƙasashen Iraƙ da Afghanistan kuma a yanzu haka ƙasar ke fafutukar janyewa daga wannan yanki. A baya ga haka su kansu ƙasashen Larabawa zasu yarda su ba da cikakken goyan baya bisa manufa? Kawo yanzun dai Qatar da haɗaɗɗiyar daular Larabawa ne suka bayyana shirinsu na yiwuwar ba da gudummawa. Amma fa wataƙila. Idan har ta kai ga raba ƙasar Libiya gida biyu dole gabacin ƙasar ya kasance ƙarƙashin riƙon amana, inda zai dogara kacokam akan taimako daga ƙetare. Ƙudurin na kwamitin sulhu dai ka iya zama babban ƙalubale fiye da yadda masu goyan bayansa suka yi zato da farko.

Mawallafi: Daniel Scheschkewitz/Ahmad Tijani Lawal
Edita: Mohammad Nasiru Awal