1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Rikicin kasuwanci tsakanin Amirka da Turkiyya

Suleiman Babayo
August 14, 2018

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya yi barazanar kaurace wa kayayyakin laturoni na Amirka saboda sabanin kasuwanci tsakanin kasashen.

https://p.dw.com/p/33AAS
Türkei Ankara Rede Erdogan
Hoto: picture-alliance/Xinhua/Turkish Presidential Palace

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya ya yi gargadi kan yuwuwar neman kaurace sayen kayayyakin laturoni daga kasar Amirka, yayin da kasar ta Turkiyya ta fada matsaloli inda kudin kadar na Lira ke faduwa, sakamakon rikicin kasuwanci da diplomasiyya da mahukuntan birnin Washington. A cewar shugaban 'yan Turkiyya za su iya kera kayayyakin da suke bukata da ingancin da ya fi wadanda ake kai wa zuwa kasar.

A wannan Talata darajar kudin kasar ta Turkiyya da ake kira Lira ya dan farfado bisa wasu matakan da babban bankin kasar ya dauki, bayan shiga mawuyacin hali.