1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin diplomasiyya tsakanin Chadi da Jamus

April 12, 2023

Kasashen Jamus da Chadi sun katse hulda ta diplomasiyya sakamakon rikicin da ya kunno kai tsakanin su.

https://p.dw.com/p/4PwlN
Jakada Gordon Kricke
Gordon Kricke jakadan Jamus a Chadi da aka koraHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Takun saka ya barke tsakanin kasashen Chadi da Jamus inda suka katse hulda diplimosiyya bugo guda. Duk da cewa ma dai gwamnatin N'djamena ce ta fara korar jakadan Jamus da ke kasarta tana mai zarginsa da yin katsalandan a harkokinta na cikin gida kafin sannan ita ma fadar Berlin ta mayar wa kura aniyarta inda ta ba wa jakadiyar Chadi wa'adin ficewa daga kasarta.

Karin Bayani: Chadi ta sallami jakadan Jamus da ke kasarta

Wannan tirka-tirka tsakanin gwamnatin Chadi da Jamus ta samo asali ne watanni kadan da suka gabata bayan da Jamus da sauran kasashen Yamma suka soki yadda hukumomin Chadi karkashin Mahamat Idriss Deby Itno suka yi amfani da karfin tuwo domin murkushe wata munmunaar zanga-zanga da aka gudanar a ranar 20 ga watan Oktoban bara lamarin ya yi ajalin mutane da dama. Sannan kuma Jamus da kasashen Yamma sun yi ta matsa lamba ga gwamnatin mulkin sojojan ta rikon kwarya ta Chadi da ta gaggauta dawo da kasar kan tafarkin dimokuradiyya kamar yadda yayin jawabinsa na farko bayan ya karbi ragamar iko Muhamat Idriss Deby ya alkawarta shirya zabe a cikin watanni 18, zaben da kuma ba zai tsaya takara ba.

Mahamat Idriss Deby, shugaban Chadi
Shugaba Mahamat Idriss Deby na rikon kwarya a ChadiHoto: Francois Mori/AP/dpa

To sai ba a je ko ina ba da matashin mai shekaru 38 da haihuwa ya dandana dadin mulki nan da nan sai maganar ta sauya, inda ya tsawaita wa'adin gwamnatin rikon kwarya da shekaru 2 ta hanyar wani taro na kasa da ya kira wanda ya sahale masa tsayawa takara a zaben da kasar za ta shirya. To sai dai wasu bangarori na mutanen Chadi sun kauracewa taron wanda suka ce ya yi hannun riga da dimokuradiyya. Wannan batu ya haifar da bore wanda ya kusa sake jefa kasar cikin yakin basasa. Wannan ne ma ya sa kasashe abokan huldar Chadi ta hanyar ofisoshin jakadancinsu suka ringa kokarin sauya tunanin gwamnatin sojojin kan matakin.

Matakin korar jakada Gordon Kricke ya zo wa gwamnatin Jamus da mamaki, domin dai manufofinsa daya da na sauran jakadun kasashen Yamma abokan huldar Chadi kan kudirin gwamnatin mulkin sojan kasar. Ayar tambayar da ake dasawa a nan ita ce: shin anya kuwa wannan mataki da gwamnatin sojan Chadi ta dauka ba tauna tsakuwa ne ba domin bai wa aya tsoro? To wannan magana dai tana kusa da tabbata domin a 'yan watannin nan ofisoshin jakadancin kasashe da ke birnin N'djamena sun dan ja baya da harkoki ba kamar ba yadda aka saba gani a baya ba ciki har da na kasashen Tarayyar Turai irin su Sifaniya, Holand, Birtaniya, Faransa da Jamus sannan kuma da na Amurka, kuma hakan na tabbatar da kama hanyar lalacewar hulda tsakanin Chadi da kasashen masu yi wa sojoji matsin lamba kan shirinsu na ci gaba da rike madafun iko

Mariam Ali Moussa
Mariam Ali Moussa jakadiyar Chadi a Jamus da aka koraHoto: Dean Calma/IAEA/Wikipedia

Jamus dai ba ta sanar da sake sabon jakada a kasar Chadi ba tun bayan dawowar Gordon Kriche gida, to amma fadar Berlin ta rama wa kura aniyarta inda ta bai wa jakadiyar Chadi Mariam Ali Moussa wa'adin sa'o'i 48 daga jiya Talata (11.04.2023) na ta tattara an tsanake ta fice daga kasar.

Wannan tirka-tirka dai ta tsamin dangataka da ta kuno kai a tsakanin Chadi da Jamus ta sake buda mahawara kan yadda alakar wasu kasashen Afirka dake karkashin mulkin sojoji da kasashen Yamma ke lalacewa kamar dai yadda Mali da Burkina Faso suka kori sojoji har ma da jakadun Faransa. Ayar tambayar da ake dasawa a nan ita ce: shin wai kasashen Afirka sun fara gajiya ne da bin umurnin manyan kasashe uwayen gidansu?