1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Take hakkin dan Adam a Koriya ta Arewa

February 17, 2014

Cikin wani rahoton bayan bincike da ta gudanar mai shafuka 372, Majalisar Dinkin Duniya ta zargi gwamnatin Koriya ta Arewa da laifin azabtarwa da kuma kashe 'yan kasarta.

https://p.dw.com/p/1BAeY
Hoto: Reuters

Kwararrun masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun fitar da wani rahoto a kan keta hakkin bil Adama a Koriya ta Arewa, inda suka zargi shugaba Kim Jong Un da yin amfani da mukaminsa wajen cin zarafin 'yan kasarsa. Wanda ya shugancin wannan kwamitin bincike Michael Kirby ya nunar da cewa daruruwan manyan jami'an gwamnati na da hannu wajen tursasa wan 'yan Koriya ta Arewa. a kuma kara da cewa ba dade ko ba juma shi shugaban da mukarrabansa za su iya fuskantar shari'a saboda laifin azabtarwa da kashe kashen bil adama da ka iya kaiwa ga kisan kare dangi.

Ita dai gwamnati Koriya ta Arewa ta yi watsi da rahotan mai shafuka 372, ta na mai dangantashi da wata manakisa da abokan gabanta ciki har da Amirka da Koriya ta kudu da Japan suka shirya don bata mata suna a duniya. Ita ma dai China da ke dasawa da Koriya ta Arewa ta ce za ta hau kan kujerar naki idan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi yunkurin gurfanar da shugabannin Koriya ta Arewa gaban kotun hukunta manyan laifukan yaki da ke birnin The Hague.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar