1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takarar Jam'iyyar 'Yan uwa Muslmai a Masar

April 30, 2011

Ƙungiyar Yan uwa Musulmi ta ƙasar Masar ta rikiɗa zuwa jam'iyyar siyasa domin tsayawa takara a zaɓen watan Satumba

https://p.dw.com/p/116zx
Alamar Ƙungiyar 'Yan uwa Musulmai

A ƙasar Masar ƙungiyar 'Yan uwa Musulmai wato Muslim Brotherhood ta ce za ta shiga zaɓen 'yan majalisa da zai gudana a watan Satumban bana. Ƙungiyar a yau ta naɗa kakakinta Muhammad Al-Masri a matsayin jagorar sabuwar jam'iyar da ta kafa, mai suna Freedom and Justice ko kuma Yanci da Adalci. Sabon jagorar ya ce sabuwar jam'iyar tasu ba ta da alaƙa da matsanancin ra'ayi na addini ko wata manufa da ba ta demokraɗiyya ba. Ƙungiyar 'Yan uwa Muslmai dai ita ce ƙungiyar adawa mafi tsari da haɗin kai a ƙasar ta Masar, duk da cewa an shafe shekaru ana ta tozartar ta da mambobinta. Tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Mubarak, ƙungiyar ke jawo hankali masu gudun kasancewarta mai ƙin hada kai da waɗanda ke da sassauci.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Halima Balaraba Abbas