1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takarar Bola Tinubu na fama da cece-kuce a Najeriya

Ubale Musa M. Ahiwa
December 5, 2022

A Najeriya hankali ya karkata a kan kauracewar da dan takarar jam'iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya yi daga wata muhawara mai tasiri a zaben 2023.

https://p.dw.com/p/4KV4g
Dan takarar ar shugaban kasa a Najeriya, Bola Tinubu
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi

Daya bayan daya dai an kai ga muhawara kusan guda hudu, a cikin nazarin masu takara ta shugaban kasar a zabukan badi. To sai dai kuma har ya zuwa yanzu babu keya ta dan takara ta jam'iyyar APC mai mulki da ke fatan dorawa bisa mulkin kasar. A wasu lokuta dai Bola Tinubun na ban hakuri tare da kauracewa jerin muhawarar, a yayin kuma da a wasu yake fitowa fili, shi da magoya baya wajen dawowa daga rakiyar masu shirya muhawarar da ake nunawa kai tsaye ta kafafen labaru na kasar.

Kauracewar Tinubun da ke zaman daya a cikin masu takara na kan gaba cikin fagen siyasar kasar dai na jawo fassara daban-daban cikin fagen siyasar Najeriyar.

An kamalla wata muhawarar a Abuja, tare da Tinubun kasancewa a cikin birnin Landan, kuma a fadar Sulaiman Kadade, da ke zaman shugaban matasan jam'iyyar PDP ta adawa, kuskure ne babba ga dan takarar na jam'iyyar APC ya tsallake kasar zuwa waje a yayin da kasa ke fatan saurare daga gare shi.

Nigeria l APC Ergebnis l Präsidentschaftskandidat
Hoto: Nigeria Prasidential Villa

A bana kuma a karon farko dai kungoiyi da yawa sun shirya muhawarar da fatan ji a bangare na masu neman mulkin a wani abin da ke zaman ba sabunba. Kuma a fadar Abdullahi Tanko Yakasai da ke jagorantar kungiyar kwarraru na arewacin Najeriya cikin jam'iyyar APC, Tinubun ya shirya tsaf da nufin halartar muhawara daya tilo ta kungiyar kafafen labaran kasar.

Ko bayan yakin neman zaben da ke zaman matattara ta masu siyasar Najeriyar da nufin aiken sako dai, muhawara ta kafafen zumunta na zamani hanya mafi farin jini tsakanin miliyoyin ‘yan kasar da ke neman tantance aya cikin tsakuwa ta siyasar ta kasar. Kuma a fadar Faruk BB faruk da ke sharhi kan batun na siyasa dabarar Tinubun na iya kaiwa ya zuwa kai shi ga matsala cikin kasar da al'ummarta ke bukatar neman hanya ta ficewa a cikin jerin matsalolin da ke ta tarnaki ga rayuwa da ci gaban kasa.