1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Takaddamar Orano da gwamnati

Gazali Abdou Tasawa LM
December 4, 2024

Takun sakar da aka kwashe watanni ana yi tsakanin gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar da kamfanin Orano na kasar Faransa mai aikin hakar uranium, ya dauki sabon salo.

https://p.dw.com/p/4nkZH
Nijar | Orano | Uranium | Takaddama
Takaddama na kara karfi tsakanin gwamnatin mulkin sojan Nijar da kamfanin OranoHoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

Sabon salon rikici tsakanin gwamnatin mulkin sojan Nijar da kamfanin Orano na kasar Faransa mai hakar uranium dai, na zuwa ne bayan da hukumomin sojan sun girke sojoji a cikin kamfanin uranium din kasar na Somair wanda Orano ke da sama da kaso 64 cikin 100 na hannun jarinsa. Sai dai tuni matakin ya soma haifar da muhawara a tsakanin 'yan kasar ta Nijar, inda wasu ke ganin dacewarsa wasu kuma na ganin akasin hakan. Wannan matakin dai ya biyo bayan dakatar da aikin hako uranium din sabili da kasa fitar da shi domin sayarwa kasuwar duniya da kamfanin na Orano ya yi sakamakon rufe kan iyaka, matakin da gwamnatin Nijar din ta ki amincewa da shi. A share daya kuma tuni gwamnatin ta fara zawarcin kasar Rasha, kan ta zo ta zuba jari a aikin hakar uranium din kasar.

Nijar | Orano | Uranium | Takaddama
Takaddamar kamfainin Orano na Faransa da gwamnatin mulkin sojan NijarHoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

Da yake tsokaci kan matakin girke sojoji a kamfanin na Somair, Malam Ismael Mohamed na kungiyar Debout Nijar cewa ya yi lokaci ya yi da Nijar din za ta karbe kamfanin tare da mallaka wa kasa shi baki daya. To amma wasu 'yan kasar na ganin wannan mataki na amfani da karfin soja lokacin da ake takaddama da kamfanin, ba hanya ce mai bulle wa ba. Shi ma Malam Moustapha Abdoulaye wani mai sharhi kan harkokin yau da kullum a Nijar din, na ganin akwai bukatar bangarorin biyu su bi hanyar diplomasiyya wajen warware wannan rikicin a maimakon amfani da karfi. Kawo yanzu dai gwamnatin mulkin sojan ta Nijar ba ta yi wani bayani game da dalilanta na girke jami'an tsaro a cikin kamfani na Somair ba, kuma jama'a sun zura ido su ga yadda za ta kaya tsakanin gwamnatin mulkin sojan da kamfanin na Orano.