CDU da CSU a Jamus na cigaba da takaddama
June 15, 2018'Ya'yan jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun musanta wani rahoto da ke cewa an yi kira ga shugaban majalisar dokokin kasa Wolfgang Schäuble da ya shiga tsakani don yin sulhu tsakanin jam'iyyun kawance na CDU da CSU a kan batun 'yan gudun hijira.
'Yan siyasa daga jam'iyyar CDU sun ce ba a nemi Schäuble don ya taimaka a samu maslaha a takaddamar da ake yi tsakanin jam'iyyun biyu kuma kawayen juna wato CDU da CSU kan manufar gwamnati da ta shafi yin kaura da hijira a kasar ba.
Bambancin ra'ayi da ya kamari tsakanin Merkel da ministan cikin gida kuma shugaban jam'iyyar CSU Horst Seehofer kan batun na 'yan gudun hijira na barazanar ruguza gwamnatin 'yan ra'ayin mazan jiya da yanzu ke jan raganmar gwamnatin hadin gwiwa da jam'iyyar SPD a Jamus.
A wannan Jumma'a jaridar Rheinische Post ta ruwaito cewa jam'iyyar CDU na ganin Schäuble a matsayin mutumin da sassan biyu ke mutuntawa dangane da adawarsa da manufofin Jamus kan 'yan gudun hijira a da da kuma yadda yake biyayya da Merkel sau da kafa.