1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan mallakar kogin Nilu

June 7, 2013

Kasar Masar ta yi barazanar amfani da karfin soja don hana hukumomi a Habasha aiwatar da aikin gina madatsar ruwa a kogin na Nilu.

https://p.dw.com/p/18lkF
A picture taken on May 28, 2013 shows the Blue Nile in Guba, Ethiopia, during its diversion ceremony. Ethiopia has begun diverting the Blue Nile as part of a giant dam project, officials said on May 29, 2013 risking potential unease from downstream nations Sudan and Egypt. The $4.2 billion (3.2 billion euro) Grand Renaissance Dam hydroelectric project had to divert a short section of the river -- one of two major tributaries to the main Nile -- to allow the main dam wall to be built. 'To build the dam, the natural course must be dry,' said Addis Tadele, spokesman for the Ethiopian Electric Power Corporation (EEPCo), a day after a formal ceremony at the construction site. AFP PHOTO / WILLIAM LLOYD GEORGE (Photo credit should read William Lloyd-George/AFP/Getty Images)
Hoto: William Lloyd-George/AFP/Getty Images

Bari mu fara da jaridar Der Tagesspiegel wadda a labarinta mai taken „Yakin mallakar kogin Nilu“ ta mayar da hankali a kan katafaren aikin gina wata madatsar ruwa da kasar Habasha ke yi a kogin Nilu, abin da ya harzuka kasar Masar har tana barazanar daukar matakan soji.

Jaridar ta ce rikicin ya faro ne lokacin da gwamnati a Addis Ababa da sauran kasashen dake iyaka da wuraren da ruwan kogin ke kwarara suka janye daga wata yarjejeniya da ta samo asali tun lokacin mulkin mallaka. A wancan lokaci turawan mulkin mallakar Birtaniya sun ba wa Masar ikon hana yin duk wani aikin datse ruwan kogin, matakin da tun da farko lokacin Habasha dake zama tushen kogin, ba ta amince da shi ba. Masar dai ta ce ba za ta taba yin watsi da ‚yancinta na tarihi ba. Yanzu haka dai wannan rikici ya koma tsakanin Habasha da Masar. Tun a cikin watan Maris shekarar 2011 makonni hudu bayan kifar da gwamnatin Hosni Mubarak, Habasha ta girka harsashin gina madatsar ruwa, wadda ta ba wa wani kamfanin kasar Italiya kwangilar aikin. A halin da ake ciki hukumomi a birnin Alkahira na tunanin amfani da karfin soja don hana aiwatar da wannan aiki, yayin da takwarorinsu na birnin Addis Ababa suka ce a shirye suke sun tunkari dakarun na Masar.“

Bauer mit Bewässerungsanlage für den Maisfeld in Kwadiya Dorf bei Dutse, Jigawa, Nigeria. 29.03.2013, Kwadiya, Jigawa / Nigeria Copyright: DW
Hoto: DW

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tsokaci ta yi kan cimaka tana mai nuna da cewa an inganta matakan samar da abinci mai gina jiki a duniya, sannan sai ta ci gaba kamar haka.

Bunkasar hanyoyin samar da abinci a duniya

„A rahoton da ta bayar ranar Talata hukumar abinci da aikin gona ta Majalisar Dinkin Duniya FAO ta ce an samu gagarumin ci-gaba wajen samar da abinci a duniya, inda yanzu kashi 12.5 cikin 100 na al'ummomin duniya ke fama da karancin abinci idan aka kwatanta da kashi 50 cikin 100 a shekarar 1947. Rage yawan masu fama da yunwar dai gagarumin aiki ne da ya cancanci yabo. Sai dai har yanzu a wasu yankuna na duniya musamman a kasashe masu tasowa na Afirka Kudu da Sahara da kuma wasu yankuna na nahiyar Asiya ana fama da matsalar karancin abinci, musamman masu dauke abubuwa masu gina ciki ga yara kanana.“

Ladar kudi a kan 'yan ta'addar Afirka ta Yamma

Tukwici ga wanda ya taimaka aka kai ga kame shugabanin Al-Kaida a yammacin Afirka inji jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai rawaito cewar ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta ware kudi kimanin dala miliyan 23.

This image taken from video posted by Boko Haram sympathizers shows the leader of the radical Islamist sect Imam Abubakar Shekau made available Wednesday Jan. 10, 2012. The video of Imam Abubakar Shekau cements his leadership in the sect known as Boko Haram. Analysts and diplomats say the sect has fractured over time, with a splinter group responsible for the majority of the assassinations and bombings carried out in its name. (AP Photo) THE ASSOCIATED PRESS CANNOT INDEPENDENTLY VERIFY THE CONTENT, DATE, LOCATION OR AUTHENTICITY OF THIS MATERIAL
Ladar dala miliyan bakwai ga wanda ya kamo Imam Abubakar ShekauHoto: AP

"A karon farko Amirka ta ware miliyoyin daloli a zaman tukwici ga wanda ya ba da bayanai game da shugabannin kungiyoyin 'yan ta'adda, inda kaso mafi yawa za a ba wa wanda ya kamo ko ya ba da bayanan da za su kai ga cafke shugaban kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram a Najeriya wato Abubakar Shekau. A cikin sanarwar ma'aikatar harkokin wajen ta Amirka, wadanan kungiyoyin na da alaka da kungiyar Al-Kaida reshen yankin Magreb da sojojin sa kai na kungiyar Al-Shabaab ta Somaliya sai kuma kungiyar Al-Kaida ta yankin tsibirin kasashen Larabawa. Wannan matakin da Amirka ta dauka na daga cikin shirinta mai sunan "Rewards for Justice" wato Lada don adalci, wanda ta bullo da shi tun a shekarar 1984."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe