1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan kudin motocin 'yan majalisa

Ramatu Garba Baba
July 23, 2021

Gwamnatin Shugaba Yoweri Museveni a Yuganda na shan suka kan raba wa 'yan majalisar kasar sama da dala miliyan 30 don siyan motocin hawa.

https://p.dw.com/p/3xwIP
Uganda I Parlamentswahlen
Hoto: Parliamentary Press Office/Uganda

Takaddama ta kaure a kasar Yuganda, bayan da gwamnatin Shugaba Yoweri Museveni, ta raba ma 'yan majalisan kasar sama da dala miliyan talatin don siya musu motoci. Kowanne daga cikin 'yan majalisan kasar da suka haura dari biyar, ya sami akalla dala dubu hamsin da shida a farkon wannan makon.

Masu sukar matakin gwamnatin, sun baiyana damuwa kan halin da kasar ta ke ciki na karancin allurar riga-kafin corona a daidai lokacin da kasar ke fuskantar barazana daga sabon nau'in corona mai suna Delta a zagaye na biyu. 

Wasu na zargin gwamnati da yin almubazarranci da kudadenm kasa. Suna cewa, babu wani mataki, na a zo a gani, da gwamnatin Shugaba Yoweri Museveni ta dauka na dakile cutar, baya ga ayyana dokar kulle, kasar na ci gaba da fama da karancin kayan aiki a asibitoci da suka cika makil da masu fama da corona, a yayin da sauran al'ummar kasar ke kukan karancin kayayyakin kare kai daga kamuwa da cutar mai kama numfashi.