1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China na sa ido a harkar Taiwan

Yusuf BalaJanuary 18, 2016

Sakatare janar na jam'iyyar DPP Joseph Wu ya tafi kasar Amirka a ranar Litinin din nan bayan da mahukuntan birnin Beijing ke ci gaba gargadin Taiwan ta manta da batun neman ballewa.

https://p.dw.com/p/1Hf9B
Jaushieh Joseph Wu
Sakataren jam'iyyar DPP Joseph WuHoto: picture-alliance/dpa/dpaweb

Wani babban mamba daga jam'iyyar da ke fafutikar 'yancin Taiwan daga China zai ziyarci Amirka bayan da jam'iyyarsu ta DPP ta samu gagarumin rinjaye a zaben da ya gudana a karshen mako, wani lamari da ke nuna kullewar dangantaka tsakanin kawayen juna yayin da Amirkar ke zame wa Taiwan wurin samun makamai.

Ziyarar ta sakatare janar na jam'iyyar ta DPP Joseph Wu wacce ya tafi kasar ta Amirka a ranar Litinin din nan, na zuwa ne bayan da mahukuntan birnin Beijing ke ci gaba gargadin Taiwan ta manta da batun neman ballewa .

Jam'iyyar Tsai Ing-wen ta DPP dai ta samu gagarumin rinjaye a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa da ya gudana a karshen mako, wani abu da ya sake nuna shiga sabuwar tankiya da China wacce ke bayyana cewa koda da karfin tuwo ba za ta bari yankin na Taiwan ya kubuce mata ba.