Taba Ka Lashe: 12.08.2015
August 14, 2015Talla
A tarayyar Najeriya manyan shehunan malaman harshen Hausa ne suka baje kolin iliminsu a nazarin wakokin Hausa a yayin taron "ga fili ga mai doki" na bana da sashen nazarin harsunan Nijeriya a Jami'ar Bayeru ta Kano ke shiryawa a ko wace shekara, inda ake gayyato mawaka su baje kolin su su kuma manazarta su yi nazarin wakokin tare kuma da fede su.