1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina ta ruwaito sabbin kamuwa da corona

Zainab Mohammed Abubakar
June 14, 2020

Chaina da Koriya ta Kudu sun ruwaito mafi yawan sabbin wadanda suka kamu da cutar corona tun watanni biyu da suka gabata, batu da ke haifar da fargaba tsakanin al'umma.

https://p.dw.com/p/3djyD
China Peking Xinfadi Markt geschlossen
Hoto: Reuters/M. Pollard

Hukumomomin lafiya a Jamus, sun sanar da cewar an  samu karin mutane 247 da suka kamu da cutar Covid-19. Wannan ya kawo adadin yawan wadanda coronar ta kama zuwa sama da dubu 180, daga cikinsu sama da dubu takwas sun mutu.

A halin da ake ciki kuma, Masar ta sanar da mafi yawan wadanda suka kamu da cutar ta Covid-19, fiye da yadda aka saba gani a kullum.

Ana kara samun karuwar yaduwar cutar tsakanin wasu jihohin Amurka, a daidai lokacin da shugaba Donald Trump ke kara matsa kaimi don ganin an bude harkokin kasuwanci, duk da gargadin kwararru a fannin lafiya.

Cikin tsukin sao'i 24, Chaina ta tabbatar da corona a jikin mutane 57, a cewar hukumar lafiya ta kasar da cutar ta samo tushe. Adadin da ke zama mafi yawa tun daga tsakiyar watan Afrilu, da annobar ta yi sauki.