1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaFaransa

Ta yaya makamai za su bai wa Faransa karin kudaden shiga?

October 10, 2024

Faransa na shirin fadada hanyoyin samun kudaden shigarta a fannin kere-keren kayan yaki, ta la'akari da abin da Shugaba Emmanuel Macron ya sanar tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamaya a Ukraine a shekarar 2022.

https://p.dw.com/p/4ld2T
Jirgin yaki kirar Faransa
Jirgin yaki kirar FaransaHoto: abaca/picture alliance

Faransa ta fi kowace kasa kashe kudi a fannin ayyukan soji a nahiyar Turai. To sai dai ana aza ayar tambaya kan har zuwa wani lokaci ne hakan zai sauya tattalin arzikin kasar, kuma wani tasiri zai yi ga ma'aunin tattalin arzikinta da ma samar da ayyukan yi.

A yanzu haka wani kamfanin sarrafa jirage marasa matuka mai suna Delair na gwajin wasu jirage marasa matuka, masu saukin sarrafawa da ke amfani da wasu sassa da ake samu a ko ina a duniya. A baya bayan nan, kamfanin ya samar da jirage marasa matuka na bincike guda 150 ga Faransa, inda gwamnatin Paris ta aika wa dakarun Ukraine da ke filin daga.

Wannan dai na kasancewa daga wani bangare na shirin Shugaba Macron na fadada hanyoyin samun kudaden shigar kasar a fannin kere-keren kayan yaki, a wani mataki na inganta fannin kera makamai na cikin gida domin samar da da katafaren masana'antar kera makamai a Turai. Sai dai kuma masu sukar lamirin gwamnatin Macron na cewa, wannan yunkurin nasa ba shi ne ya kamaci Faransa a wannan lokacin ba.

Kamfanin kera jiragen marasa matuka na da niyyar samar da kusan dukannin abun da ake bukata a yanzu. Ta nunka abin da take samu a shekara zuwa Euro miliyan 30 a shekarar bara, kana kamfanin ya dauki a kalla mutane 120 aiki har sau biyu cikin shekaru biyu da suka gabata. Sai dai kuma shugaban kamfanin ya ce wasa farin girki.

A yanzu dai kamfanin na son kara habaka ayyukansu ta hanyar kara yawan kudin da yake samu a duk shekarar zuwa euro miliyan 100 dama yawan ma'aikartansa nan da shekarar 2027.