071209 Dialog Ausstiegsprogramme
January 7, 2010Talla
Tun a cikin watan Afrilun shekara ta 2008 aka kafa wata gidauniya a birnin London mai suna Quilliam Foundation inda masu matsanancin ra´ayin addinin Musulunci da suka yi watsi da wannan ra´ayi ke taimakawa don yaƙi da tsauraran aƙidoji a cikin addinin. Kasancewa masu wannan namijin aiki a yanzu sun san irin kalamai na yaudara da hanyoyin da ake amfani da su wajen shawo kan matasa su rungumi tsattsauran ra´ayin addini, ya sa sun ɓullo da na su dubarun domin kuɓutar da matasan daga hannun masu amfani da addini don biya wasu bukatu na su.