1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddamar Rasha da Amirka akan makomar Siriya

July 4, 2012

Rasha ta ce babu tattaunawar da za ta yi da Amirka akan saukar Assad daga mulkin Siriya .

https://p.dw.com/p/15R9i
U.S. Secretary of State Hillary Rodham Clinton meets with Russian Foreign Minister Sergey Lavrov, in St. Petersburg, Russia, June 29, 2012. REUTERS/POOL/Haraz N. Ghanbari (RUSSIA - Tags: POLITICS) - eingestellt fab
Clinton da LavrovHoto: Reuters

A wannan Larabar ce gwamnatin ƙasar Rasha ta yi watsi da rahotannin da ke cewar tana gudanar da tattaunawa tare da ƙasar Amirka akan tayin baiwa shugaban Siriya Bashar al-Assad mafakar siyasa a matsayin wata hanyar kawo ƙarshen watanni 16 da aka yi ana zubar da jini a ƙasar, wanda kuma ya janyo mutuwar fiye da mutane dubu 16 da 500. Muƙaddashin ministan kula da harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov ya shaidawa kanfanin dillancin labaran ƙasar Rasha na Interfax cewar tattaunawar da ƙasashen biyu suka yi sam-sam ba ta taɓo yanayin da ake ciki a Siriya da kuma makomar shugaba Assad ba.

Dama wata jaridar da ake bugawa kowace rana a ƙasar Rasha ta Kommersant ta ambaci wata majiyar diflomasiyyar Rasha na cewar ƙasashen yammacin duniya a ƙarƙashin jagorancin Amirka na ƙoƙarin shawo kan Rasha ta amince da baiwa Assad mafakar siyasa.

Sai dai kuma rahoton da jaridar ta buga ya ƙara da cewar mahukunta a birnin Moscow na ƙasar Rasha sun yi watsi da tayin, kana a yanzu muƙaddashin ministan harkokin wajen na Rasha ya ce ƙasar sa na yin adawa da shiga tsakanin ƙetare a matsayin hanyar warware rikicin na ƙasar Siriya, wadda ke zama ƙasa ɗaya tilon da ta rage da dangantakar ƙut-da-ƙut tare da ita a yankin Gabas Ta Tsakiya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu