1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama a masarautar Zinder tsakanin 'yan sarki

July 7, 2011

Gwamnatin Nijar ta maido da tsohon sarki Abubakar Sanda da aka tsige daga muƙamin shekaru goma da suka wuce

https://p.dw.com/p/11r4o
Sarki Aboubacar Oumarou Sanda da aka sake naɗawa a DamagaramHoto: DW

Masarautar' Damagamaram a Jamhuri'ar Nijar ta shiga cikin wani rikici na jayayya bayan da hukumomi suka sake dawo da tsofon sarkin. Masana tarihi da al'adu na yin fashin baƙi akan ta'ƙaddamar da ta kuno kai

An dai soma gudanar da bincike akan tsofon sarkin ne Abubakar Sanda wanda yanzu aka mayar da shi akan gadon sauratar, bisa zargin yin zangon ƙasa ga gwamnati da safarar miyagun ƙwayoyi da aikata kisan gilla tare da yin fataucin motocin sata da kuma yin amfani da kuɗin jabu a ranar 10 ga watan Yuni na shekara ta 2001 kafin daga bisani ministan cikin gida na waccan lokaci ya ba da ummarnin a tsige shi daga masayin sarkin a ranar tara ga watan Yuli na shekara ta 2001.

Sannan kuma aka kama shi aka kulle a gidan kurku tare da wani wanda ake dangantawa da haɗa baki da shi wato Zakari Oumaro na ɗaurin tsawon shekaru biyu a gidan kurku na garin Kolo a shekara ta 2002. Kana kuma aka tilasta ma su biyan kuɗaɗen diyya jika ɗari biyu na kuɗin CFA da kuma mayar da kuɗaɗe kimanin miliyan 21 da aka tuhume su da sacewa mallakar gwamnati.

Bayan dai tsohon shekaru biyu na zaman kaso a garin Kolo an sako sarki Abubakar Sanda a ranar 20 ga watan Maris na shekara ta 2003. An dai sauke sarkin ne a lokacin mulkin ƙawance na Tanja Mamadou da kuma Mahaman Ousman tsofon kakakin majalisar dokokin wanda ya fito daga jihar ta Zinder, wanda kuma a wani lokacin ake baza jita jitar cewar ba su ɗasa wa da tsofon sarkin. Kuma a yanzu a mayar da shi Abubakar Sanda akan gadon sarautar a zuwan tsofuwar jam'iyar adawar ta ƙasar kan karagar mulki wato PND Tarraya

Wannan dai ya sa jama'a suna aza ayar tambaya cewa anya kuwa ba siyasa a cikin wannan batu

Dakta Ado Mahaman malamin jami'a ne a Nijar

''A'a ba zan iya ce ma ka babu siyasa a cikin batun ba amma abinda na sani shi ne cewa shara'a ce ta sake mayar da shi akan gadon sarautar''.

To sai dai akan wannan batu da yanzu haka yake ɗaukar hankalin al'umar ƙasar Farfesa Djbo Hamani malamin tarihi a jami'ar Abdoulmoumuni Diffo ta birnin Yamai ya yi tsokacin cewa

''Mutane su daina cewa akwai siyasa cikin wannan al'amari, a Nijar tun lokacin turawa ake tsige sarakuna, kuma sarakuna suna a ƙarƙashin ikon gwamnati a ko da yaushe gwamnati na da ikon sauke sarki ta naɗa wanda ta ke buƙata ya yi sarautar.

Babban fargabban da ake da shi dai akan wannan al'amari na masarautar Zinder wacce ke da daraja da kuma mahimmanci a ƙasar ta Nijar ka da kuma bayan ficewar waɗannan hukumomi wasu kuma idan suka zo su sake tsige sarkin ko kuma su kawo wani sauyi

Farfesa Djibo Hamani ya ce akwai mafita:

''Ya cancanta a girka wata doka da za ta magance irin waɗanan matsaloli, a koma ga yin amfani da tsofuwar al'ada ta wakilta wasu mutanen da kan iya naɗa sarki.''

Aboubacar Oumarou Sanda, Sultan von Damagaram/Niger
Sarki Mahamadou Moustapha Kakali da aka sauke daga sarautar DamagaramHoto: DW

Shi dai sarki Moustafa Kakali da aka tsige daga gadon sarautar ya ce shi ne sarki na farko da aka zaɓa a Zinder domin kuwa duk sauran sarakuna naɗasu ake yi.

Kuma a irin wannan rikici na 'yan sarki idan ya tashi Allah kaɗai Ya san irin waibuya da sidabaru na jefe jefe da ake samu daga sassa daban daban saboda wataƙila rashin imani na danganta canjin al'ammura da kan zo ga bil Adama daga indallahi. Kuma har yazuwa yanzu gwamnatin ƙasar Nijar ɗin ba ta ce ufan ba dangane da rikicin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Ahmad Tijani Lawal