1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An haramta wa 'yan adawa taron gangami a Sénégal

Abdoulaye Mamane Amadou
December 30, 2023

Gwamnatin Sénégal, ta haramta taron gangamin siyasar da zai tsayar da madugun 'yan adawa Ousmane Sonko takara a zaben shugabancin kasar

https://p.dw.com/p/4aimN
Senegal I Babban birnin Dakar I Masu goyoyn bayan Ousmane Sonko
Senegal I Babban birnin Dakar I Masu goyoyn bayan Ousmane SonkoHoto: JOHN WESSELS/AFP/ Getty Images

Hukumomi a birnin Dakar na kasar Sénégal, sun haramta taron gangamin da 'yan adawar kasar da suka kudri anniyar gudanarwa a wannan Asabar. 'Yan hamayyar sun ce a yayin taron ne gangamin siyasar ne za su tsayar da takarar Ousmane Sonko, a zaben shugabancin kasar da ke tafe a karashen watan Febrairun 2024.

Masu ruwa da tsaki a harkokin mulkin Sénégal da suka tabbatar da haramcin gangamin wa kamfanin dillancin labarai na AFP, sun bayyana cewa suna fargabar taron ka iya rikidewa ya zama wata tarzoma, lamarin da 'yan adawar suka musanta.

An shafe tsawon watanni ana ta kai ruwa rana game da takarar Ousmane Sonko, bayan zarginsa da aikata laifukan da ka iya haramta masa tsayawa takara a babban zaben kasar ta Sénégal, zarge-zargen da madugun 'yan adawar ya sha musantawa.