1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rattaba hannu a yarjejeniyar sulhu

Zainab Mohammed Abubakar
December 5, 2022

Shugabannin soji da farar hula sun rattaba hannu kan yarjejeniyar da ke da nufin kawo karshen rigingimun da suka mamaye Sudan tun bayan kifar da mulkin kasar a bara.

https://p.dw.com/p/4KVXz
Sudan Khartoum | Abkommensunterzeichnung - Abdel Fattah al-Burhan
Hoto: AFP via Getty Images

A watan Oktoban 2021 ne dai hafsan soji Abdel Fattah al-Burhan ya kwace mulki, matakin da ya tarwatsa kokarin da ake yi samar da gwamnatin farar hula tun bayan kifar da tsohon shugaban kasar mai dogon zamani Omar al-Bashir a 2019.

Cikin shekara guda da ta gabata dai, Sudan din ta fuskanci zanga-zangar adawa a kusan kowane mako, da kamen masu fafatukar neman kafuwar demokradiyya.  Alkaluman jami'in kiwon lafiya na nuni da mutane 121 sun rasa rayukansu, daura da matsi na tattali da rigingimun kabilanci da suka barke a wasu yankunan Sudan din.