1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tarwatsa masu adawa da soji a Sudan

Abdul-raheem Hassan
November 7, 2021

Jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa zanga-zangar malamai a wajen ma'aikatar ilimi da ke Khartoum, inda suke nuna adawa da juyin mulkin sojoji.

https://p.dw.com/p/42h1P
Sudan | Pro Demokratie Proteste in Khartoum
Hoto: Marwan Ali/AP/picture alliance

Zanga-zangar ta biyo bayan kiran da wata kungiyar kwadago, na bijirewa umarnin gwamnati tare da yin watsi da tayin raba madafun iko da sojoji. Kungiyar kwadon da ta kira zanga-zangar ta taka rawa sosai a zanga-zangar 2018 zuwa 2019 da ya kai ga hambarar da tsohon Shugaban kasar Omar al-Bashir a watan Afrilun 2019.

Masu zanga-zangar sun yi barazanar shiga yajin aiki na tsawon kwanaki biyu fara daga ranar Lahadi. Tun bayan juyin mulkin ranar 25 ga watan Oktoba na shekarar 2021, aka fara zanga-zangar kin jinin mulkin soji a Sudan, akalla mutane 14 ne aka kashe tare da raunata kusan 300, a cewar likitocin Sudan.