1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta kudu za ta fice daga Heglig

April 20, 2012

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu ya yi alƙawarin hanzarta janye dakarunsa da suka mamaye yankin heglig na sudan kamar yadda ƙasashen duniya suka bukata.

https://p.dw.com/p/14iOx
BRUSSELS, March 20, 2012 President of South Sudan Salva Kiir Mayardit speaks during a press briefing after meeting with President of European Commission Jose Manuel Barroso (not seen) at the EU headquarters in Brussels, capital of Belgium, March 20, 2012
Salva Kiir na rikici da al-BashirHoto: picture alliance / ZUMA Press

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu ya bayyana cewar ya bai wa sojojin ƙasarsa izinin janyewa daga yankin Heglig ta Sudan da suka mamaye tun kwani goman da suka gabata. Cikin wata sanarwa da kakakin gwamnati ya karanta lokacin wani taron manaima labarai da ya gudana a Juba  babban birni, shugaban na sudan ta kudu ya nunar da cewar nan da kwanaki uku masu zuwa dakarunsa za su gama tattara nasu ya nasu domin ficewa daga yankin na kan iyaka tsakanin makobtana biyu da ke rikici da juna.

Wannan matakin da salvir kiir ya ɗauka ya biyo bayan nuni da shugabanni daban daban ciki har da sakatare na majalisar Ɗinkin Duniya suka yi cewar mamaye yankin Heglig da Sudan ta kudu ta yi ya saɓa da dokokin ƙasa da ƙasa. Da ma kuma ƙasar Sudan ta yi barazanar kifar da gwamantin kudancin Sudan mai ci yanzu matiƙar ta ci gaba da takalarta da faɗa. wannan yanki na Heglig ya ƙunshi rabin albarkatun man fetur da Sudan ta ke trinƙaho da shi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halimatu Abbas